Gwamnatin ƙasar China 🇨🇳 ta ce babu wani wuri a cikin yarjejeniyar ba Nijeriya 🇳🇬 rancen Dala miliyan $500 ya saka ƴancin Nijeriya na zama cikakkiyar ƙasa.
A lokacin da majalisar Wakilan Nijeriya ke bincike kan karɓo bashin, ta yi zargin cewa yarjejeniyar ta haɗa ƴancin Nijeriya na zama ƙasa, a cikin kadarorin mallaka idan har ba a biya bashin ba.
Saidai kuma ma’aikatar wajen China ta ƙaryata zargin a wata sanarwa da ta fitar tana mai cewa ƙasar ba ta da wannan shirin.
