Ƙasashen Afirka na kashe kusan dala biliyan 90 a duk shekara wajen biyan basussukan ƙasashen, yayin da suke sake biyan wasu dala biliyan 75 a matsayin ƙarin ruwa sakamakon tsadar rancen da ake bai wa nahiyar.
Babban sakataren harkokin wajen Kenya, Korir Sing’oei, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Nairobi yayin rufe taron karo na shida kan bashi da ci gaban Afirka (AfCoDD VI), wanda AFRODAD ta shirya.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Sing’oei ya ce tsadar bashi na tilasta wa gwamnatocin Afirka yin zaɓi mai wahala tsakanin biyan basussuka da kuma kashe kuɗi kan kiwon lafiya, ilimi da kare al’umma daga illolin sauyin yanayi.
Ya ce ƙarin dala biliyan 75 da Afirka ke biya a matsayin ruwa ya samo asali ne daga abin da ya kira ƙarin kuɗin da ake ɗora wa ƙasashen nahiyar, wanda ya bayyana a matsayin “harajin amana”.
A cewarsa, Afirka na bukatar kusan dala tiriliyan 1.3 a duk shekara domin cimma muradun ci gaba mai ɗorewa. Ya kuma ce kusan kashi 60 cikin 100 na mafi kyawun albarkatun hasken rana na duniya na Afirka ne, amma nahiyar na samun kusan kashi ɗaya cikin 100 kacal na kuɗaɗen makamashi mai tsafta.
Batun bashi ya shafi Nijeriya ma, inda ma’aikatar kuɗi ta ce ƙasar ta kashe ƙarin Naira tiriliyan 10.61 wajen hidimar bashi tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025. Mafi yawan ƙarin kuɗin, wato Naira tiriliyan 9.37, ya samo asali ne daga faduwar darajar Naira da tasirinsa kan biyan bashin waje.
Sing’oei ya ce tsarin bashin Afirka ya sauya sosai, inda a shekarun 1990 kusan kashi 70 cikin 100 na bashin nahiyar ke hannun masu ba da bashi na Paris Club, yayin da a yanzu kusan kashi 40 cikin 100 ke hannun masu mallakar takardun bashi masu zaman kansu.
Ya ce sauyin ya sa tattaunawar sake fasalin basussuka ta ƙara rikitarwa, yana mai cewa tsadar rance ta zama muhimmin batu da ya kamata a duba a manufofin harkokin wajen Afirka, ba wai a bar shi ga ma’aikatun kuɗi da baitulmalin ƙasashe kaɗai ba.
