Home Labarai Bashin da ake bin Nijeriya ya kai ₦27.4tn

Bashin da ake bin Nijeriya ya kai ₦27.4tn

135
0

Alƙalumma daga ofishin kula da basukan Nijeriya DMO, sun nuna cewa bashin da ake bin gwamnatin tarayya, jihohi 36 da Abuja ya kai ₦27.4tn a watan Disambar 2019.

Wannan dai ya nuna an samu ƙari a bashin da ake bin ƙasar daga watan Satumbar bara, lokacin da aka bayyana yawan sa a ₦26.22tn.

Bashin ƙasar na ₦27.4tn, ya haɗa da basukan cikin gida da na waje, wanda gwamnatin tarayya da jihohi suka ciyo.

Bayanan da aka samu daga ofishin na DMO a jiya Laraba ya nuna cewa bashin cikin gida ya kai ₦18.3tn kwatancin kashi 67.07 kenan na yawan bashin da ake bin ƙasar.

Gwamnatin tarayya na da yawan bashin cikin gida da ya kai ₦14.2tn yayin da jihohi da Abuja ke da ₦4.1tn.

Yawan bashin ƙasashen waje da ake bin Nijeriya kuwa na ₦9.02tn kashi 32.93 kuwa, gwamnatin tarayya na da bashin ₦7.5tn yayin da jihohi da Abuja ke da ₦1.4tn.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply