Kwamitin zabe na kungiyar Northern Nigeria Writers’ Summit karkashin jagoranci Odoh Diego Okenyodo ya bayyana Dr. Bashir Abu Sabe a matsayin sabon shugaban kungiyar Northern Nigeria Writers’ Summit.
A ranar Litinin 16-11-2020 kwamitin mai dauke da mutum uku, ya bayyana Dr. Abu Sabe a matsayin wanda ya yi nasarar lashen zaben da sauran mukaman da aka yi takarar a kansu.
Dr. Bashir Abu Sabe Babban Malami (Senior Lecturer) ne a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua da ke Katsina. Ya yi digirinsa na farko da na biyu a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, ya samu digirinsa na uku a Jami’ar Alkhahira da ke Masar.
Ya yi rubuce-rubucensa kan abin da ya shafi adabin kasuwar Kano da kuma kamanci da bambancin da ke akwai tsakanin marubuta mata a kasar Masar da Nijeriya.
Masani ne kan nazarin adabin Hausa a fannoni da dama. Shi ne shugaban kungiyar Marubuta ta kasa reshen jihar Katsina. Ya taba zama dan kwamiti na taron NNWS a 2017 da aka yi a Katsina.
Dr. Abu Sabe yana da kishi da son rubutu da marubuta da adabi gabadaya, ya bayar da gudunmawarsa sosai wajen ci gaban rubuce-rubuce ta fuskoki daban-daban.
KUNGIYAR TUNTUBA TA MARUBUTAN AREWACIN NIJERIYA (NORTHERN NIGERIA WRITERS’ SUMMIT)
An kafa wannan kungiya a Minna da ke jihar Niger a 2008 wadda ta zama inwar marubutan Arewacin Nijeriya na jihohi 19 da ke Arewa, da nufin tsare-tsaren cigaban marubutan yankin. A shekara ta 2018 a Maiduguri, jihar Borno aka kafa shugabancin riko karkashin shugabanta Malam Baba M. Dzukogi, da suka tafiyar da kungiyar.
JADAWALIN SHUGABANNIN DA AKA ZABA
Dr. Bashir Abu Sabe -Chairman
Omale Allen Abduljabbar -Vice Chairman
Safiya Isma’il Yero. -Secretary
Isma’il Bala Garba -Asst. Secretary
Hussaini Kado -Treasurer
Awaal Gata -PRO (North Central)
Haruna Adamu HAdejia -PRO (North West)
Yusuf Garba Yusuf -PRO (North East)
Maryam Gatawa -Auditor
Ogbe Benson Aduojo Esq -Legal Adviser
Tee Jay Dan -Ex-Officio 1
Dr. Bashir Abu Sabe ya cancanci rikon wannan kungiya, muna yi masa fatan alheri, tare da addu’ar Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da aka dora masa, amin.
