Home Labarai Batan kudin Alhazai: EFCC ta yi dirar mikiya kan hukumar alhazan Kebbi...

Batan kudin Alhazai: EFCC ta yi dirar mikiya kan hukumar alhazan Kebbi kan N90m

74
0

Hukumar yaki da cin hanci ta Nijeriya EFCC ta yi dirar mikiya kan hukumar jin dadin Alhazan jihar Kebbi, saboda rashin mayar da N90m ga mahajjatan jihar na shekarar 2017/2018.

Shugaban hukumar mai kula da jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara Abdullahi Lawal ya tabbatar da haka a yau Litinin.

A cewar sa hukumar ta yi nasarar samun kudade a lokacin samamen da ta kai a hukumar.

Ya kara da cewa yanzu haka sun gayyaci shugaban kwamitin mayar da kudaden, da Daraktan kudin hukumar domin amsa tambayoyi.

Lawal ya yi bayanin cewa hukumar aikin haji ta kasar ce NAHCON ta mayarwa mahajjatan shekarar 2017/2018 kudaden ta hanyar hukumomin alhazan na jihohi, amma babu wata shaida da ke nuna jami’an na jihar Kebbi sun mayar da kudin ga alhazan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply