Home Kasashen Ketare Bayan bayyanar Jong-un Amirka za ta ci gaba da tattaunawar nukiliya da...

Bayan bayyanar Jong-un Amirka za ta ci gaba da tattaunawar nukiliya da Korea

168
0
Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya sake tabbatar da ƙoƙarin fadar Washington kan warware shirin makaman nukiliyar Korea ta Arewa tare da samar da kyakkyawar gobe ga mutanen ta, bayan da shugaban Korea ta arewar Kim Jong-Un ya sake bayyana kwanaki 20 bayan ya yi ɓatan dabo.
Da yake zantawa da ABC News a makon nan, Pompeo ya bayyana musayar wutar da aka yi a Korea sau biyu, baya bayan nan, a matsayin akasi, a daidai lokacin da fargaba ke ƙaruwa a tsakanin jama’a cewa wannan zai gurgunta tattaunawar da ake da fadar ta Pyongyang.
A ranar Asabar ne dai kamfanin dillancin labaran Korean Central News ya ruwaito cewa Kim, ya halarci taron buɗe wani kamfanin takin zamani a arewacin Pyongyang, wanda ya kawo ƙarshen jita-jitar da ake yaɗawa kan yanayin lafiyar sa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply