Home Wasanni Bayan janye zargi guda har yanzu ana tuhumar Blatter

Bayan janye zargi guda har yanzu ana tuhumar Blatter

94
0

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Sepp Blatter ya ce wani dan kasar Suwizalan da ke bincike kan kan yadda ya bada wata kwangilar talabijin ya janye.

Saidai FIFA ta ce wannan ba shi ke nuna an wanke shi daga zarge-zargen ba.

Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Talata Blatter mai shekaru 84, ya ce ofishin mai gabatar da kara na tarayya sun sanar da shi cewa sun rufe binciken badakalar.

Ya ce labarin wanda ke zuwa shekara biyar bayan ya sauka daga mukamin shugaban FIFA saboda zarge-zargen, labari ne mai kyau.

Babban lauyan gwamnatin kasar dai ya janye tuhuma daya daga cikin biyu da ake yiwa Blatter tun a shekarar 2015 kan zargin rashin nuna adalci da kuma cin amana.

Saidai hakan na nuni za a ci gaba da binciken sa kan biyan Euro miliyan 1.88 ga Michel Platini tsohon shugaban hukumar UEFA kuma wakili a gwamitin gudanarwar FIFA.

Blatter dai ya yi murabus ne a ranar 2 ga watan Yunin 2015, kwanaki hudu bayan ya yi nasarar sake zama shugaban na FIFA a karo na biyar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply