Home Sabon Labari Ondo2020: Card Reader ya ba dan takarar Gwamna na PDP matsala ta...

Ondo2020: Card Reader ya ba dan takarar Gwamna na PDP matsala ta awanni biyu

134
0

Ɗan takarar gwamnan jihar Ondo a ƙarƙashin jam’iyyar PDP Eyitayo Jegede ya kaɗa ƙuri’arsa, bayan shafe kimanin sa’a biyu, na’urar tantance masu zaɓe, (Card Reader) na ba su matsala.

Jegede ya zo runfar zaɓensa tun misalin ƙarfe 9 na safe inda ya shafe kusan awa biyu a kan layi saidai kuma da layi ya zo kan su, na’urar ta kasa tantance katin zaɓensa da na matarsa.

A nan ne kuma aka faɗa masa na’urar na da matsala kafin daga bisani a shawo kan matsalar.

Akwai ‘yan takara da ke neman kwace mulki daga hannun jami’iyyar APC mai mulkin jihar. Sai dai fafatawa tafi zafi a tsakanin Ɗan takarar jam’iyyar APC kuma gwamna mai-ci Rotimi Akeredolu da dan takarar jam’iyyar PDP mai adawa Eyitayo Jegede.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply