Home Kasashen Ketare Bayan shekaru 40, Iran ta sahale wa mata shiga kallon kwallon kafa

Bayan shekaru 40, Iran ta sahale wa mata shiga kallon kwallon kafa

129
0

Abdullahi Garba Jani

Bayan kusan shekaru 40, mata a kasar Iran sun samu damar shiga filin wasan Azadi na birnin Tehran don kallon wasan kwallon kafa.

Iran dai ta kara da kasar Cambodia ne a wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin duniya. Rahotanni suka ce an samu mata daga 3,500 zuwa 4000 da suka sayi tikitin shiga kallon wasan.

Matan dai sun shiga wurin da aka ware musu don su kalli wasan da mata ‘yansanda da likitoci ne kawai suka shiga filin. ‘Yan kallo da magoya baya dai sun yi ta busa da kururuta ‘yan wasan kasar ta Iran.

Tun bayan juyin-juya halin musulunci da aka yi a kasar Iran ne dai aka haramta wa mata shiga kallon wasanni a kasar duk kuwa da matsin lamba da aka yi ta samu.

A baya dai, har wasu suna yin shigar-burtu su saka gemun karya su yi shiga irin ta maza don su samu damar shiga filin wasa. Ko a watan Satumba sai da wata mata ta mutu, bayan da ta cinna wa kanta wuta bayan da ta ji haushi an hana ta shiga kallon wasan kwallon kafa.

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA na ganin wannan dage doka da aka fara yi a kasar a matsayin babbar nasara. Shugaban hukumar Gianni Infantino sai da ma ya yi barazanar hana kasar Iran shiga gasar cin kofin duniya na shekarsr 2022 a kasar Qatar muddin kasar ba ta dage wannan doka ba.

Amma dai dage dokar ya tsaye kan wasannin da suka shafi gasar cin kofin duniya amma ban da wasannin cikin kasar Iran.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply