Home Labarai Bayan tsawon lokaci Ali Nuhu ya bayyana ƴarsa Fatima

Bayan tsawon lokaci Ali Nuhu ya bayyana ƴarsa Fatima

918
0

A karon farko Jarumi Ali Nuhu ya wallafa wani hotonsa tare da babbar ƴarsa Fatima a shafinsa na Facebook.

An dai ɗauki lokaci mai tsawo ba a ji ɗuriyar Fatima ba, wadda a baya ta fara haskawa a fina-finan Hausa kuma daga bisani ta yi ɓatan dabo.

Hakan dai ya janyo cecekuce, ta yadda wasu ke ganin Ali Nuhu ya hana ƴar tasa shiga harkar fim ne saboda ta fara tasawa, inda saidai ƙanenta Ahmed Ali Nuhu ake gani.

Ali Nuhu ya wallafa hotonsu tare da Fatima, sannan ya rubuta “My beautiful daughter Fatima” Ma’ana: kyakkyawar ɗiya ta Fatima.

A daidai lokacin da jaridar Dclhausa ta ga wannan hoto da jarumi Ali Nuhu ya sanya mutane 7600 suka so hoton, sannan mutane 784 suka tofa albarkacin bakin su sai kuma mutane 49 waɗanda suka rarraba hoton bayan sanya shi da mintuna 56.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply