Home Sabon Labari Bayelsa 2019: Diri ya lashe zaben fitar da gwani na PDP

Bayelsa 2019: Diri ya lashe zaben fitar da gwani na PDP

70
0

Nuruddeen Ishaq Banye

 

Sanata mai wakiltar mazabar Bayelsa ta tsakiya a majalisar dattawan Nijeriya Douye Diri, ya lashe zaben fitar da gwani na gwamnan jihar da jam’iyyar PDP ta gudanar.

 

Da yake bayyana sakamakon zaben a safiyar yau Laraba, shugaban kwamitin zaben kuma gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku, ya ce Diri ya samu kuri’u 561 inda ya doke babban abokin takarar sa Timi Alaibe wanda ya samu kuri’u 365, da sauran ‘yan takara 19.

 

Diri dai, shi ne dan takarar da yake samun goyon bayan gwamna Seriake Dickson na jihar, kuma a ranar Litinin ne daren jajibirin zaben fitar da gwanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a kananan hukumomi 18 na jihar suka amince da mara masa baya.

 

Diri ya taba zama dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Yenagoa/Kolokuma/Opokuma, tsakanin shekara ta 2015 zuwa 2019, kafin a zabe shi a matsayin sanata mai wakiltar Bayelsa ta tsakiya a babban zaben da ya gabata a karkashin jam’iyyarsa ta PDP.

 

A ranar 16 ga watan Nuwamba ne ake sa ran hukumar zaben Nijeriya za ta gudanar da zaben gwamna a jihar ta Bayelsa. Kuma fafatawa za ta fi zafi a tsakanin Mr. Douye Diri na jam’iyyar PDP mai mulkin jihar da kuma wanda jam’iyyar APC za ta tsayar a matsayin dan takararta.

Majiyarmu: Banye/dkura

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply