Home Sabon Labari Bayelsa 2019: Lyon ya zama ɗan takarar APC

Bayelsa 2019: Lyon ya zama ɗan takarar APC

109
0

Hannatu Mani Abu/Banye

David Lyon ya zama tsayayyen ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa da za a gudanar, bayan ya lashe zaɓen fidda gwani da aka sanar da sakamakon sa.

Lyon ya samu kuri’u 42,138 wanda ya ba shi damar lashe zaben tare da tserewa abokan takarar sa fintikau.

Sauran ƴan takarar da aka gwabza da su a zaben fidda gwanin sun hada da Heineken Lokpob wanda ya samu kuri’u 571, da Preye Aganaba mai kuri’u 354, da Amgbare mai kuri’u 633, da Maureen Etebu mai kuri’u 564 sai kuma Diseye Nsirim wanda ya samu kuri’u 1,533.

Da yake bayyana sakamakon zaben Dangana Emmanuel, wanda shi ne shugaban masu tattara sakamakon zaben ya ce an gudanar da zaben fidda gwanin a bisa ka’ida kamar yadda aka tsara kuma kwamitin jam’iyyar a matakin kasa suka tabbatar.

Kamfanin Dillancin labaru na Nijeriya NAN, ya ruwaito cewa jam’iyyar APC ta yi amfani da salon zabe na kai tsaye wajen fidda gwanin wanda zai fafata da sauran jam’iyyu a zaben gwamnan jihar na ranar 16 ga watan Nuwamba. Fafatawa za ta fi zafi a tsakanin shi  Mr Lyon da wanda jam’iyyar PDP ta tsayar a matsayin dan takararta domin jihar Bayelsa jiha ce da ke hannun PDP mai adawa. Kuma masu sharhi na ganin sai an kai ruwa rana kafin a samu wanda zai lashe zaben gwamnan.

NAN, ya bayyana cewa gwamnan jihar Yobe Mai-mala Buni shi ne jami’in bayar da sakamako a zaben fidda gwanin na jam’iyyar APC a jihar ta Bayelsa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply