Home Sabon Labari Bayelsa: APC na cikin yanayin da ka iya ruguza ta ko bunkasa...

Bayelsa: APC na cikin yanayin da ka iya ruguza ta ko bunkasa ta

63
0

Hannatu Mani Abu/Jani

A ranar Asabar mai zuwa ne jam’iyyar APC a jihar Bayelsa za ta gudanar da zaben fidda gwani cikin ‘yan takarkari wadanda za a gwabza da su a zaben kujerar gwamnan jihar.

A yanzu dai akwai kimanin mutane takwas masu neman kujerar gwamnan jihar a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Koda yake ana ganin zaben zai fi zafi ne tsakanin tsohon ministan aikin gona Sanata Heineken Lokpobiri da wani babban dan kasuwa David Lyon.

Akwai tsohon gwamnan jihar Timipre Sylva wanda a baya yana daga cikin ‘yan takarar kafin shugaba Buhari ya nada shi karamin ministan albarkatun man fetur.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply