Home Sabon Labari Bayelsa: ba ido rufe nake neman matsayin gwamna ba-Alaibe

Bayelsa: ba ido rufe nake neman matsayin gwamna ba-Alaibe

65
0

Rahma Ibrahim Turare

 

 

Mai neman jam’iyyar PDP ta tsayar da shi dan takarar gwamna a jihar Bayelsa Mr Timi Alaibe  ya ce ba zai taba amincewa da duk wani rikici ko tada hankullan jama’a ba don ya samu gwamnan jihar.

 

Mr Alaibe ya yi wannan bayanin ne a Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa, inda ya ce yanke hukunci da ya yi na ya tsaya takarar wannan kujera ya biyo bayan tsananin soyayyar da ya ke yi wa mutanen jihar Bayelsa.

 

Za a dai gudanar da zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP  a ranar 3 ga watan Satumba. Yan takara 21 ne za su fafata a wannan zabe don a fitar da wanda zai yi wa jam’iyyar ta PDP takarar gwamna.

Tsohon Shugaban Nijeriya Goodluck tare da Gwamna Dickson na jihar Bayelsa. Wadannan mutanen sune jiga-jigan PDP a Bayelsa a yanzu

Mr Alaibe ya ci gaba yana cewa ko a  zabukan da suka gabata ya sha janyewa yana bar wa wasu takarar domin kauce wa tashin hankali na siyasa.

 

Ya ce baya da wata karuwa ko alfahari idan har za a  zubar da jinin dan jihar  Bayelsa don kawai ya zama gwamna.

 

Ya ce yana daya  daga cikin wadanda suka fuskanci matsala ta siyasa, inda har hari aka taba kai masa.

 

 

 

 

Sahara reporters:        Rahma/Jani

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply