Home Tsaro BB Naija na nuna jima’i -inji kungiyar Musulunci

BB Naija na nuna jima’i -inji kungiyar Musulunci

96
0

Fim din Batsa na BBNaija: KUNGIYAR MUSULUMCI TA CE BBNAIJA NA NUNA JIMA’I BABU TSORON ALLAH.

Shugaban kungiyar MURIC, Kungiyar kare yancin musulman Najeriya, farfesa Ishaq Akintola ya ce fim din BBNaija wanda wasu gidajen talabijin ke nuna wa a DSTV da GoTV na nuna jima’i karara ga jamaar Najeriya har da kananan yara.

Farfesa Akintola yace fim din ya kan nuna wasu na jima’i a “filin-Allah-Ta’ala” ba tare da boye wani abu ko jin kunya ba.

Fim din na BBNaija da akafi sani da fim na zahiri na tattaro matasa suyi gasa akan wasu abubuwa a zahiri ciki kuwa har da jima’i idan ta dauro. A karshen gasar duk matashi ko matashiyar da suka nuna gwaninta za a basu kudi kamar Naira Milyan 50, abinda shugaban kungiyar kare yancin musulman yace wannan Milyan 50 ba abin murna bace domin nan bada jimawa ba fim din zai tarwatsa tarbiyyar jamaar Afrika wadanda ba a sansu da nuna jima’i a bayyanar jama’a ba.

A saboda haka Malamin addinin yace DOLE gwamnati ta dauki matakin hana ci gaba da sanya wannan fim a Najeriya. Yace rashin tarbiyya da badala basu san addini ba, a don haka ya na bukatar kiristoci ma su sa hannu wurin tilasta gwamnati dakatar da wannan fim.

#ZuD

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply