Home Kasashen Ketare Biden da Harris ne gwarazan shekara na mujallar TIME

Biden da Harris ne gwarazan shekara na mujallar TIME

122
0

Mujallar TIME ta kasar Amirka ta bayyana zababben shugaban Amirka Joe Biden tare da mataimakiyarsa Kamala Harris a matsayin gwarazanta na shekarar 2020 da take shirin karewa.

“Editan TIME Chief Edward Felsenthal ya fada a wata sanarwa cewa mujallar ta zabi Joe Biden da Kamala Harris a matsayin gwarazanta ne bisa yadda suka sauya siyasar kasar a babban zaben kasar da aka gudanar a watan Nuwamban shekarar nan.

Biden ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaba Barack Obama, yayin da Harris ta zama mace ta farko kuma bakar fata da za ta zama mataimakiyar shugaban kasa a Amirka.

Yanzu dai ya rage Kasa da kwanaki 40 a rantsar da Joe Biden da Harris a matsayi waɗanda za su shugabanci kasar ta Amirka.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply