Shugaban ƙasar Amirka Joe Biden ya soke wasu dokokin tsohon shugaban ƙasar Donald Trump da suka shafi sauyin yanayi da kuma shiga ƙasar, a ranarsa ta farko da kama aiki.
Daga cikin dokoki 17 da Biden ya zartas a ranar Laraba sun haɗa da soke haramcin shiga Amirka da aka sanyawa ƙasashen Nijeriya, Eritrea, Yemen, Sudan da sauran ƙasashe.
A lokacin da yake sa hannu ga dokokin Biden ya ce babu lokacin ɓata wa, kuma wannan shi ne farko ga abubuwan da zai yi.
