Home Kasashen Ketare Biden zai ba baƙin haure daga Mexico damar shiga Amirka

Biden zai ba baƙin haure daga Mexico damar shiga Amirka

28
0

A ranar Juma’ar nan ne, Gwamnatin shugaba Joe Biden na Amirka ta bada sanarwar cewa za a fara shigo da ‘yan ci ranin da aka tilasta wa zama Mexico wadanda aka warware matsalolinsu a Amirka daga makon gobe.

A farkon watannan ne dai Biden ya umurci sashen kula da tsaron kula da iyakokin kasar ya kawo karshen shirin nan na tilasta ‘yan ci ranin zama Mexico wanda tsohon shugaban kasar Donald Trump ya kirkiro.

Wannan mataki dai ya tilasta ‘yan gudun hijiran da ba ‘yan Mexico ba, wadanda yawancinsu daga Amirka ta tsakiya suke, aka kora su, kafin fitowar bukatun da suka mika na neman shiga kasar, wanda hakan ya haifar da matsalar kai agaji a yankin biyo bayan barkewar cutar Covid-19.

Wata sanarwa da hukumar tsaron iyakokin kasar ta fitar, ta ce za ta fara kashin farko na shirin samar da tsarin ba ‘yan ci ranin damar shigo wa Amirka daga iyakar kasar ta Kudu maso Yamma, a ranar 19 ga watan Fubrairu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply