Home Labarai Bikinn Easter: Gwamnatin Nijeriya ta bada hutu a ranakun Juma’a da Litinin

Bikinn Easter: Gwamnatin Nijeriya ta bada hutu a ranakun Juma’a da Litinin

48
0

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a 10 da Litinin 13 ga watan nan na Afrilu a matsayin ranakun hutun Easter na shekarar 2020.

Ministan harkokin cikin gida Ra’uf Aregbesola ya bayyana hakan, inda yayi kira ga mabiya addinin kirista dake kasar nan da su yi koyi da kyawawan halayen Yesu Almasihu da suka hada da juriya da soyayya da zaman lafiya da kuma jinkai.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar Georgia E. Ehuria ya sanyawa hannu, Aregbesola ya yi kira a gare su da su yi amfani da wannan damar wajen yiwa Najeriya da ma fadin duniya Addu’a kan yayewar annobar cutar Covid-19.

Kazalika ministan ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da marawa kokarin da Gwamnatoci ke yi wajen yaki da annobar cutar Coronavirus.

Ya kuma tunatar da su kan bukatar dake akwai na su bi dokokin da hukumomi ke sanyawa domin kare yaduwar cutar a kasar, musamman abinda ya shafi bada tazara da tsafta da sauran su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply