Home Labarai Binciken Magu: Duk wanda ya ci, sai ya yo amai – Buhari

Binciken Magu: Duk wanda ya ci, sai ya yo amai – Buhari

153
0

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yaƙi da cin hanci da rashawa a kasar, ba zai tsallake kan duk wanda aka bincika aka tabbatar da ya yi ba dai-dai ba.

Kan haka ne Buhari ya ce babu wani wanda ya isa ko ake shakkun hukuntawa a kasar, matsawar an same shi da danne dukiyar al’umma.

Ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke karbar rahoton kwamitin Ayo Salami wanda ya binciki Ibrahim Magu kan zargin azurta kai da kuma laifin yi wa kudin da ya kwato a hannun barayin gwamnati, abin nan da ake kira sata-ta-saci-sata.

Buhari ya ce ran sa ya baci matuka da aka wayi gari ana zargin hukumomin da aka nada su dakile cin hanci su na harkalla da kudade da kadarorin da su ka kwato.

Muryar ‘Yanci ta rawaito cewa Buhari ya ce an kafa kwamitin Ayo Salami bisa yadda dokar kafa kwamitin bincike ta 2004 ta shimfida.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply