Home Labarai Binta Masari ta tallafi daliban makarantar Kankara

Binta Masari ta tallafi daliban makarantar Kankara

228
0
Hajiya Hadiza Aminu Masari

Mai dakin gwamnan jihar Katsina Binta Aminu Bello Masari ta raba wa daliban makarantar Kankara da aka sace tallafin kudi Naira dubu goma-goma.

Hajiya Hadiza Aminu Masari

Hajiya Binta da ta samu wakilcin kwamishinan matasa da wasanni Sani Danlami ta bayyana tallafin a matsayin abin da zai kara kwantar da hankalin yaran da kuma iyayensu.

Ta shaida wa DCL Hausa cewa, gwamnatin jihar Katsina a shirye take ta ba ilimi kariya a kodayaushe domin shi ne gishirin zaman duniya da ginshikin cigaban al’umma.

A jawabinsa, shugaban sashen mulkin karamar hukumar Kankara Nura Alasan Machika ya yaba wa mai dakin gwamnan akan wannan tallafi da ta ba daliban, ya kuma gode wa gwamnatin Masari bisa kokarin da take na ganin ta shawo kan matsalar tsaro a fadin jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply