Home Kasashen Ketare Birtaniya: Sabon Firaiminista ya nada ‘yar Nijeriya a matsayin minista

Birtaniya: Sabon Firaiminista ya nada ‘yar Nijeriya a matsayin minista

91
0

Daga Zaharaddeen Umar

 

Sabon Firamainistan Birtnaiya Boris Johnson ya nada Olukemi Olufunto Badenoch a matsayin ministar Harkokin Yara da Iyali ta Birtaniya kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

An haifi Olukemi Olufunto Badenoch a birnin Landan. Iyayenta kuma Yarbawa ne ‘yan Nijeriya ta kuma taso a brinin Legas na Nijeriya daga bisani tayi rayuwa a kasar Amirka. Daga nan ta koma Birtaniya inda aka haifeta. Ayanzu ta yi shekaru 16 tana zaune a Landan.


Matashiyar mai shelkaru 39 an zabe ta a matsayin ‘yar majalisa a Birtniya mai wakiltar yankin “Saffron Walden” a shekara ta 2017.

Olukemi dai ta kware a bangaren fasahar zamani ta kwamfyuta kuma tana cikin jam’iyyar Conservative mai mulkin Birtaniya.

Firaiministan Birtaniya Boris Johnson

Nadin Olukemi na cikin kokarin Firaiminista Boris Johnson na kafa gwamnati bayan da a makon da ya gabata aka zabe sa a matsayin sabon Firaiministan kasar a karkashin jam’iyyar sa ta Conservative.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply