Home Kasashen Ketare Birtaniya ta ƙwace kadarorin Yahya Jammeh

Birtaniya ta ƙwace kadarorin Yahya Jammeh

61
0

Birtaniya ta kakaba wa tsohon shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh takunkumi a wani kokari na fada hana shiga kasar da kuma kakaba takunkumin tattalin arziki ga wadanda ake zargi da take hakkin bil’adama a fadin duniya a ranar alhamis.

Tsohon shugaban wanda kayen zaben da ya sha hannun Adama Barrow a watan Disambar 2016 ya tilasta masa guduwa daga kasar, na daya daga cikin mutane uku daga Yammacin Afirka da Birtaniya ta saka a jerin mutane goma da ta saka wa takunkumin a fadin duniya.

Yanzu haka dai kasar ta haramta wa Jamme, da matarsa Zineb da tsohon babban daraktan leken asirin Gambia Yankuba Badjie shiga kasar da kuma kwace kadarorinsu.

Gwamnatin ta London ta ce Jammeh na da hannu a ririta wurar tsanar juna, kisan gilla, satar jama’a, azabtarwa, fyade da sauran ayyukan take hakkin bil’adama a shekarar 1994, lokacin da ya kifar da gwamnatin kasarsa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply