Home Labarai Boko Haram: Amnesty ta goyi bayan binciken ICC kan Sojoji

Boko Haram: Amnesty ta goyi bayan binciken ICC kan Sojoji

84
0

Ƙungiyar Amnesty International ta yi maraba da matakin kotun hukunta manyan laifuka ta ICC na binciken sojojin Nijeriya bisa zargin aikata laifukan yaƙi, a faɗan da suke da Boko Haram.

A cikin wata sanarwa da Daraktan bincike da harkokin shari’a na ƙungiyar a Nijeriya Netsanet Belay ya fitar a ranar Juma’a, Amnesty ta ce wannan wani babban mataki ne da zai buɗe kafar binciken rashin kyautatawar sojojin Nijeriyar.

Sanarwar ta yi kira ga ICC ta gaggauta fara binciken don gano aika-aikar sojojin a rikicin Arewa maso Gabashin ƙasar domin samar da adalci ga waɗanda abun ya shafa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply