Home Labarai Zulum ya jagoranci jana’iza, manoman da BH ta kashe sun kai 70

Zulum ya jagoranci jana’iza, manoman da BH ta kashe sun kai 70

129
0

Gidan rediyon Faransa ya ruwaito a ranar Lahadin nan cewa adadin manoman da Boko Haram ta hallaka a jihar Borno a ranar Asabar ya kai 70. A gefe guda kuma rahotanni sun nuna yadda Gwamna jihar Babagana Umara Zulum ya halarci jana’izar manoman da ‘yan ta’addar suka kashe.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana takaicinsa kan kisan da aka yi wa manoman shinkafan a yayin da suke tsaka da aiki a yankin Zabarmari, karamar hukumar Jere a jihar Borno.

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa ta bangaren yada labarai Garba Shehu ya fitar, inda shugaban ya yi Allah wadai da wannan aika-aika. Sai dai galibin ‘yan Nijeriya yanzu na mayar wa da shugaba Buhari martani mai zafi, suna zarginsa da gaza yin katabus, inda da ya nuna alhini sai ya kasa daukar matakin sake faruwar irin hakan a gaba. To amma a kodayaushe fadar shugaban Nijeriyar na jaddada irin muhimmancin da shugaban yake ba wa harkar tsaro.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply