Home Labarai Boko Haram: Gwamna Zulum ya tsallake rijiya da baya

Boko Haram: Gwamna Zulum ya tsallake rijiya da baya

339
0

Gwanman jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya tsallake rijiya ta baya a wani harin kwanton-bauna da mayakan Boko Haram su ka kai masa a Arewacin jihar Borno.

Rahotannin da wadanda ke cikin tawagarsa suka bayar, sun tabbatar da cewa Gwamna Zulum ya tsira daga harin ba tare da wani abu ya same shi ba.

DW Hausa ta rawaito cewa yanzu haka dai tawagar Gwamnan ta isa Munguno domin ci gaba da ziyarar aiki da ya ke yi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply