Home Labarai Boko Haram na ƙara ta’azzara a jihar Nasarawa – Gwamna Sule

Boko Haram na ƙara ta’azzara a jihar Nasarawa – Gwamna Sule

51
0

Habbakar ayyukan ta’addanci a yankunan jihar Nasarawa wanda ake zargin ƴan kungiyar Darus- Salam ne, ya sanya zaman dar-dar ga mazauna yankin da kuma gwamnatin jihar.

Jihar Nasarawa wadda ta yi iyaka da birnin tarayya Abuja, Benue da Kogi, tana fama da ƙaruwar ayyukan ta’addanci akan hanyoyi, gonaki, gidaje da kuma wuraren bauta.

Gwamna Abdullahi Sule wanda tuni ya tabbatar da samuwar kungiyar Boko Haram a jihar tasa ya bayyana cewa ƴanta’addan sun hana jihar sakat tun bayan tarwatsasu daga sansaninsu a karamar hukumar Toto inda aka ceto sama da mutum 700 da suke tsare dasu.

Gwamnan ya bayyana hakan jim kadan bayan ganawarsa da Shugaba Buhari don neman taimakon yadda za a dakile ayyukan ta’addanci a jiharsa.

Rahotanni sun bayyana cewa tsakanin 19 ga watan Janairun 2020 zuwa 18 ga Janairun 2021 an sace mutum 156 yayinda 28 suka rasa ransu ciki harda soji 7.

Ƴanta’addan sun bukaci a biya kudin fansa har milyan 109, inda aka biya milyan 44.5 don karbo wadanda aka sace a cikin shekara daya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply