Home Labarai Boko Haram sun yi garkuwa da Hakimi a Yobe

Boko Haram sun yi garkuwa da Hakimi a Yobe

140
0

Mayakan Boko Haram sun sace hakimin Maganna, Zannah Laisu Kaigama a wani hari da suka kai garin Geidam, Jihar Yobe, a ranar Laraba.

“Sun far wa garin ne cikin motoci biyar kirar Hilux, suna harbi a iska lamarin da ya sa kowa ya arce domin tsira da rayuwarsa,” inji wani mazaunin garin.

Majiyar DCL Hausa ta ce harin ya sanya firgici a zukatan mutanen garin, kasancewar mayakan sun kusa awa bakwai suna cin karen karensu ba babbaka ba tare da wata gagarumar turjiriya daga jami’an tsaro ba.

Shugaban Hukumar bada Agaji ta Jihar Yobe (SEMA), Mohammed Goje, wanda ya ziyarci garin Geidam domin gane wa idonsa irin barnar da aka yi, ya ce maharan sun lalata shaguna tare da kona wasu gidaje, suka kuma sace kayan abinci da magunguna a garin.

Ya kara da cewa maharan sun kuma dauke wata motar jami’an tsaron garin, sai dai ba a samu asarar rai ba.

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya umarci hukumar ta SEMA da ta samar da kayan tallafin gaggawa ga mutanen da harin ya shafa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply