Home Kasashen Ketare Boko Haram ta dauki alhakin kai harin Diffa da ya hallaka mutane...

Boko Haram ta dauki alhakin kai harin Diffa da ya hallaka mutane 27

202
0

A daren Asabar din nan ne wayewar Lahadi mayakan Boko Haram da aka kiyasta sun kai 70 suka afka wa garin Toumour da ke cikin jihar Diffa mai iyaka da Tarayya Najeriya.

Mutum 27 ne dai aka tabbatar sun hadu da ajalinsu a ya yin harin tare da jikkatar wadansu da dama.

Rahotanni daga yankin na nuni da cewa maharan sun cinna wa garin wuta inda sama da kaso 50 cikin 100 na kauyen ya kone kurmus.

Wannan hari dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasar ke gudanar da zabukan kananan hukumomi lamarin da ya sa aka dage zaben a yankin.

Ko a mako da ya gabata ma sai dai aka kai wani harin da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram kin ne a garin Chétimari duk dai a cikin jihar ta Diffa lamarin da ake ga wani babban kalubale ne ga sabuwar gwamnatin da zata meye gurbin gwamnatin shuga Issoufou Mahamadou da ake ga ta yi kokari wajen yaki da ‘yan ta’adda

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply