Home Labarai Boko Haram ta kashe hakimai 13 a Borno – El-kanemi

Boko Haram ta kashe hakimai 13 a Borno – El-kanemi

136
0

Shehun Borno Alhaji Garbai Elkanemi ya koka kan cewa kungiyar Boko Haram ta kashe hakimai 13, Dagattai da masu Umguwanni da dama a jihar Borno.

Shehun na Borno ya yi wannan furucin ne a birnin Maiduguri, a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kwamitin majalisar dokoki ta kasa mai kula da ayyuka na musamman karkashin jagorancin Sanata Abubakar Yusuf.

Kwamitin ya ziyarci jihar Borno ne domin duba irin ayyukan da hukumar raya yankin arewa maso Gabas ke gudanarwa.

Alhaji Garbai Elkanemi ya koka ganin yadda rikicin na Boko Haram ya yi sanadiyyar rasa rayukan dubban mutane, wasu kuma suka rasa muhallansu, suke gudun hijra a sansanoni daban-daban.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply