Home Labarai Boko Haram ta sake kai wa tawagar Zulum hari

Boko Haram ta sake kai wa tawagar Zulum hari

181
0

Mayakan kungiyar Boko Haram sun sake kai wa tawagar gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno hadi, inda suka halaka jami’an tsaro da dama.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa maharan sun kashe ‘yansanda takwas, sojoji uku, da kuma wasu mambobin kungiyar sa kai hudu da ke samun goyon bayan gwamnati a harin da aka kai kan motocin da ke dauke da gwamnan Borno Babagana Umara Zulum a kusa da garin Baga da ke gabar tafkin Chadi.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya tashi a jirgi mai saukar ungulu zuwa garin Monguno mai nisan kilomita 60, sannan ya nufi Baga a cikin ayarin motocin a karkashin tsauraran matakan tsaro.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply