Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Borno: Karin ‘yan gudun hijra 500 sun koma gidajensu

Borno: Karin ‘yan gudun hijra 500 sun koma gidajensu

139
0

Gwamnatin jihar Borno ta mayar da ‘yan gudun hijra 500 gidajensu a yanki Ajiri da ke cikin karamar hukumar Lafa ta jihar.

Gwamman jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ne ya bayyana haka, ya yin da ya ke jawabi a wajen rabon kudaden tallafi na naira dubu hamsin-hamsin ga masu karamin karfi.

Zulum ya kara da cewa ko wane gida daga cikin gidajen ‘yan gudun hijrar da su ka koma gida, za a tallafe su da buhunan Shinkafa 10 da buhun Wake 10 dama buhun garin Masara 10 da man girki, da sutura da katifu da gidajen sauro.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply