Home Coronavirus Boss bai da ikon shiga hurumin shugaban ƙasa – PDP

Boss bai da ikon shiga hurumin shugaban ƙasa – PDP

383
0

Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya PDP, ta ce sakataren gwamnatin ƙasar Boss Mustapha ba ya da hurumin bada sanarwar hukuncin shugaban ƙasa ko ƙara wa’adin dokar kulle don yaƙi da cutar Covid-19.

A ranar Litinin ne dai Mustapha, wanda shi ne shugaban kwamitin shugaban ƙasar na yaƙi da cutar, ya bada sanarwar ƙara wa’adin dokar kullen mataki na farko, da ƙarin sati biyu.

A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarun ta Kola Ologbondiyan ya fitar, jam’iyyar ta ce aikin na Mustapha ya janyo ruɗani kan ko yana da hurumin bada umarnin.

Saidai PDP ta ce sanarwar da ya bayar karya ƙa’idar mulki ne, wanda gwamnatin Buhari ta shahara a kai tun shekaru biyar da suka wuce.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply