Home Labarai Budurwa ƴar shekara 16 ta kashe kanta a Kano

Budurwa ƴar shekara 16 ta kashe kanta a Kano

218
0

Wata yarinya ƴar shekara 16 da ke aiki a wani gida a Zoo Road cikin birnin Kano mai suna Bahijja Gombe ta kashe kan ta, ranar Asabar da daddare.

Waso majiyoyi sun shaida wa Solacebase cewa Bahijja ƴar asalin jihar Gombe tana aikin sharar gida ne da tsaron shagon uwar ɗakinta, kuma ba ta zuwa makarantar Islamiyya ballanta ta Boko.

Wasu ƴan unguwar kuma sun ce an tsinci gawar yarinyar ne ta rataye kanta, da misalin ƙarfe 10pm na daren ranar Asabar, saidai sun yi zargin cewa ruwa ba ya tsami banza.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar Kano DSP Haruna Abdullahi, ya ce an kai gawar Bahijja asibitin Murtala, kuma tuni aka fara bincike don gano haƙiƙanin dalilin mutuwarta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply