Home Labarai Budurwa ta cinna wa kanta wuta a Zamfara saboda saurayinta ya gaza...

Budurwa ta cinna wa kanta wuta a Zamfara saboda saurayinta ya gaza aurenta

71
0

Wata budurwa mai suna Aisha ‘yar shekaru 17 da haihuwa ta banka wa kanta wuta a unguwarsu ta Albarkawa da ke cikin garin Gusau a jihar Zamfara.

 

Wani makwabcin gidansu Aisha ne ya shaida wa jaridar DailyTrust wannan labari. Shaidar gani da idon ya ce Aisha ta yanke shawarar  ta kashe kanta bayan da ta fahimci cewa saurayinta ba shi da kudin da zai iya biyan sadakinta.

 

Masoyan dai sun kwashe shekaru masu yawa suna soyayya amma kuma rashin kudi ya zo ya kawo cikas. Tun da farko iyayen A’isha sun kira saurayinta mai suna Umar suka ce ya kawo sadakin Naira 17,000 don a daura musu aure amma saurayin ya ce ba shi da halin samun wadannan kudade. Abin ke nan da ya hassala A’isha ta cinna wa kanta wuta kowa ya huta.

 

Bayanai sun nuna cewa A’isha ta samo galan din fetur ta antaya wa jikinta sannan ta nemo kwonkwon ashana sannan  ta banka wa kanta wuta. Cikin kankanin lokaci kuwa wuta ta mamaye mata jiki.

Shugaban ‘yan sandan Nijeriya

Rahotanni sun ce kafin A’isha ta yi wannan aika-aika sai da wata yayarta ta yi duk yadda za ta yi kada ta kunna ashanar nan amma A’siha ta ki. Bayan da ‘yar uwarta ta fusata sai ta kauce ta bar wurin, anan ne A’isha ta samu damar tafiya wani wuri na daban inda ta cinna ma kanta wuta. Sai dai daga bisani an samu wadanda suka zo aka taimaka aka kashe wutar daga jikinta.

 

Mahaifin budurwar ya ce shi dai ba shi da kudin kai ta asibiti don a lokacin da abin ya faru Naira 750 ne kawai ke aljihunsa. Amma jaridar DailyTrust ta ce a yanzu ana yiwa A’isha maganin gargajiya don a samu ta warke da kunar da ke jikinta.

 

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara SP Shehu Muhammed ya ce kawo yanzu bai samu wani bayani akan wannan labari ba, amma zai yi wa ‘yan jarida bayani idan ya samu labari a hukumance.

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply