Home Sabon Labari Buhari 🆚 Atiku: Lauyoyin kowa na fatan nasara, gobe Laraba kotu...

Buhari 🆚 Atiku: Lauyoyin kowa na fatan nasara, gobe Laraba kotu za ta yanke hukunci

144
0

[cmsmasters_row][cmsmasters_column data_width=”1/1″][cmsmasters_text]

Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaɓen shugaban ƙasa za ta yanke hukunci kan shari’a tsakanin Atiku Abubakar wanda ya yi wa jam’iyyar adawa ta PDP takarar da kuma shugaba Muhammadu Buhari wanda aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na watan Fabrairu. A ranar Laraba ne dai ake sa ran kotun za ta yanke hukunci.

 

Da ya ke jawabinsa na ƙarshe a zaman kotun, babban lauyan hukumar zaɓe ta INEC Yunus Ustaz Usman (SAN) ya ce hukumar ta gudanar da zaɓen ranar 23 ga watan Fubrairu cikin cikakkiyar biyayya ga dokar zaɓe.Ya ce wanda ke ƙara ba shi da hujjar ƙaryata hakan, a don haka ya buƙaci kotun, da ta yi watsi da shari’ar.

 

Shi ma lauyan Buhari Wole Olanipekun (SAN) ya buƙaci kotu ta yi watsi da ƙarar yana mai cewa sashi na 131 na kundin tsarin mulkin Nijeriya bai nemi a gabatar da takardar shedar kammala karatu ba.

Shugaba Buhari na APC da Atiku Abubakar na PDP

Haka zalika, lauyan APC Lateef Fagbemi (SAN) ya ce jam’iyyar PDP da Atiku, da ke zargin an tafka maguɗi a runfunan zaɓe 119,973 a mazaɓu 8,809, da ke ƙananan hukumomi 774, sun kira shaidu 62 ne kacal, kuma daga ciki biyar ne kaɗai suka kawo shaida daga rumfar zaɓe.

 

Sai dai kuma, lauyan Atiku da PDP, Levy Uzoukwu (SAN) ya buƙaci kotun, ta yi amfani da sashe na 138(1) na dokar zaɓe, da ya haramta wa duk ɗan takarar da ya yi ƙaryar tsayawa zaɓe. Ya ƙara da cewa hukuncin da kotun ƙoli ta yanke tsakanin Abdulrauf Modibbo da Mustapha Usman SC/790/2019 a ranar 30 ga watan Yuli, cewa tabbatar da cancantar ɗan takara ba batu ne na kafin zaɓe ba.

 

Haka kuma, ya ce a cikin fom CF001 da Buhari ya aike wa INEC ya ambaci takardun kammala karatu guda uku da suka haɗa da takardar firamare, da ta WAEC, da kuma ta makarantar sojoji, waɗanda duk bai sanya kwafin su ba.

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply