Home Labarai Buhari ba dan amshin shata ba ne – Fadar shugaban kasa

Buhari ba dan amshin shata ba ne – Fadar shugaban kasa

105
0

Fadar Shugaban kasar Nijeriya ta ce shugaba Muhammadu Buhari ba dan amshin Shata ba ne, wanda zai rika sanya hannu a makance kan duk abun da ya zo mashi, ko kuma yin nade-nade ga wadanda wani bangare na gwamnati ko hukumomi suka kawo masa.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Inda yake maida martani kan hashen wasu a kan tsaikon nade-naden da ya kamata a yi a bangaren shari’a.

A cewar Shehu, aikin shugaban kasar ne ya tabbatar irin wadannan nade-nade sun cimma ka’idojin da kundin tsarin mulkin kasa ya tanada domin kare dokokin kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply