Home Labarai Buhari ba zai bari a maimaita zanga-zangar EndSARS ba – Minista

Buhari ba zai bari a maimaita zanga-zangar EndSARS ba – Minista

109
0

Ministan kula da harkokin ‘yansanda Muhammad Dingyadi ya ce shugaban kasa Buhari zai yi dukkanin mai yiwuwa don ganin ba a sake maimaita zanga-zangar EndSARS ba a kasar nan.

Dingyadi ya furta haka ga manema labarai a fadar shugaban kasa Abuja bayan kammala taron majalisar tsaro ta kasa da shugaba Buhari ya jagoranta.

Yace an kira taron ne domin yi wa shugaban kasa haske dangane da halin tsaron da kasar ke ciki, da ya ke karuwa musamman a yankunan arewa maso gabas da maso yamma.

Muhammad Dingyadi ya ce a wajen taron an aminta cewa jami’an tsaro su kara zage damtse domin ganin an yi wa tufkar hanci.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply