Home Sabon Labari Buhari bai tsinana wani abu da zai iya gabatarwa a taron majalisar...

Buhari bai tsinana wani abu da zai iya gabatarwa a taron majalisar dinkin duniya ba-PDP

74
0

[cmsmasters_row data_width=”boxed” data_padding_left=”3″ data_padding_right=”3″ data_top_style=”default” data_bot_style=”default” data_color=”default” data_bg_position=”top center” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_size=”cover” data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_padding_top=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_shortcode_id=”12lusse5rv”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_bg_position=”top center” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_size=”cover” data_border_style=”default” data_animation_delay=”0″ data_shortcode_id=”xqsp2zvvnr”][cmsmasters_text shortcode_id=”qav86qk7io” animation_delay=”0″]

Jam’iyyar adawa ta PDP a Nijeriya ta ce shugaba Buhari ba ya da wani tartibin abu da zai nuna wanda ka iya amfanar Nijeriya a zauren majalisar dinkin duniya.

A karshen makon nan ne dai shugaba Buharin ya tafi birnin New York na Amirka don halartar taron Majalisar Dinkin Duniya na shugabannin kasashen duniya karo na 74.

Sai dai Sakataren watsa labarai na jam’iyyar na kasa Mr Kola Ologbondiya a cikin wata takarda ya ce shugaba Buhari zai je wannan taro ba tare da wani gagarumin kuduri na ci gaban Nijeriya ba, kuma wannan ya nuna cewa gwamnatin shugaba Buhari ba ta yin komi don ciyar da kasar nan gaba.  Jami’in PDPin ya yi zargin cewa shugaba Buhari bai amfani da damar fita kasashen waje ne don kawai wani abu na radin kansa. Ya ce hakan na faruwa ne duk da cewa shugaba Buharin zai tsaya a gaban shugabannin kasashen duniya da sauran masu ruwa da tsaki.

PDP a cikin sanarwar ta yi zargin cewa shugaba Buhari zai halarci wannan taro ne domin neman suna kawai.

Jaridar The Punch ta ruwaito jam’iyyar adawa ta PDPin ta kuma ce a cikin shekaru 4 da suka gabata haka shugaba Buhari yai ta yawo a kasashen duniya ba tare da ya kawo ma Nijeriya wani muhimmin ci gab aba daga irin wadannan tarurruka da yak e halarta.

Shugaba Buhari dai na yawan shan suka daga jam’iyyun adawa da wasu daga cikin ‘yan Nijeriya a kan yawan tafiye-tafiye da ya ke yi a kasashen waje da wasu masu sharhi kan lamurran yau da kullum ke ganin kamar barnatar da dukiyar kasa ne.

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply