Home Labarai Buhari ke da alhakin matsalolin Nijeriya – PRP

Buhari ke da alhakin matsalolin Nijeriya – PRP

73
0

Jam’iyyar PRP ta yi kira ga ‘yan Nijeriya su dora alhakin matsalolin da Nijeriya ke fuskanta kan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Jam’iyyar ta ce akwai bukatar dukkan ‘yan Nijeriya na gari su kara jajircewa wajen kwato kasar daga hannun gurbatattun shugabanni, a daidai lokacin da ‘yan kasar ke shirin shiga sabuwar shekarar 2021.

Shugaban jam’iyyar PRP na kasa Falalu Bello, wanda ya bayyana haka a sakon murnar shiga sabuwar shekara da ya aikewa ‘yan Nijeriya, ya ce gwamnatin APC ta gaza, wajen magance matsalolin da tsaro, gurguncewar tattalin arzikin kasa da kuma mawuyacin halin da jama’ar kasar ke ciki.

A cewarsa, ke fatar samun kyakkyawan yanayi a shekarar 2021, ba su taba manta kangin wahalar da suka shiga da yin nadamar salon mulkin shugaba Buhari da jam’iyyar APC tun daga shekarar 2015.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply