Home Farashin Kayan Abinci Buhari na ganawa da gwamnoni kan tsadar abinci

Buhari na ganawa da gwamnoni kan tsadar abinci

113
0

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari na wata ganawa da masu ruwa da tsaki kan hauhawar farashin kayan abinci a ƙasar.

Daga cikin mahalarta taron wand ke gudana a fadar shugaban ƙasar sun haɗa da wasu gwamnoni 6 da wakilan majalisar kul da wadatuwar abinci ta ƙasar.

Daga cikin gwamnonin akwai na jihar Kebbi Atiku Bagudu, Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos, Badaru Abubakar na jihar Jigawa, Simon Lalong na jihar Plateau, Darius Ishaku na jihar Taraba da kuma Dave Umahi na jihar Ebonyi.

Sauran masu halartar taron su ne: gwamnan babban bankin ƙasar Godwin Emefiele, sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno da wasu ministocin ƙasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply