Home Labarai Buhari na ganawar sirri da Jonathan

Buhari na ganawar sirri da Jonathan

133
0

Yanzu haka shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari na gudanar da wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

ana dai gudanar da taron ne a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Jonathan ya iso Villa ne da misalin karfe 11 na safe kuma kai tsaye ya nufi ofishin shugaban kasar.

Idan dai za a iya tunawa, kwanan nan ne kungiyar ECOWAS ta nada Jonathan a matsayin jagoran daidai rikicin siyasar Mali inda ya bada shawarar kafa gwamnatin hadin guiwa don kawo hadin kan kasar amma bangaren ‘yan adawa suka yi watsi da shawarar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply