Home Labarai Buhari ya bada umarnin kakkabe ‘yan bindiga a jihar Sokoto

Buhari ya bada umarnin kakkabe ‘yan bindiga a jihar Sokoto

102
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba sojoji umarnin kawo karshen hare-haren ta’addancin da ake yi a jihar Sokoto da ma sauran sassan Nijeriya.

Buhari ya kuma tabbatarwa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatinn tarayya a shirye take wajen kare su daga dukkan wadannan masu kashe-kashen ba gaira ba dalilin.

Shugaban kasar ya bada wannan tabbaci ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja.

Mai taimakawa shugaban kasar dai ya ce Buhari ya dauke matakinn ne biyo bayan rahoton kashe jama’ar da basu ji ba, ba su gani ba a karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto.

Shugaban kasar ya yi bayanin cewa za a yi wani gagarumin farmakin sojoji da aka yiwa taken “Operation Accord” don kakkabe ‘yan bindiga dadin da suka addabi jihohin yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Buhari wanda ya yi ta’aziyya ga wadanda suka rasa ‘yan uwan su, ya kuma yi addu’ar samun lafiya ga wadanda suka samu raunika a sakamakon hare-haren ‘yan bindigar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply