Home Labarai Buhari ya dakatar da Magu daga shugabancin EFCC

Buhari ya dakatar da Magu daga shugabancin EFCC

222
1

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya dakatar da muƙaddashin Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta ƙasar EFCC Mal. Ibrahim Magu bisa dalilin tuhumar da ake masa.

Wata majiya mai ƙarfi daga fadar gwamnatin ƙasar da ta nemi sashen hausa na BBC ya sakaya sunanta ta tabbatar da faruwar lamarin.

Tun a jiya ne dai Ibrahim Magu ya bayyana gaban kwamitin bincike da Shugaban ƙasar ya kafa ƙarƙashin jagorancin Alƙali Ayo Salami akan tuhume-tuhumen da ake masa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

Leave a Reply