Home Labarai Buhari ya gamsu da sakamakon zaben Nijar

Buhari ya gamsu da sakamakon zaben Nijar

45
0

Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ya yi zanta da shugaban kasar Nijar Muhammad Issoupou bisa yadda aka gudanar da babban zaben kasar cikin kwanciyar hankali da lumana.

Shugaba Buhari ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar, da DCL Hausa ta samu kwafi.

A zantawarsu ta wayar salula, Shugaba Buhari ya sake taya shugaban kasar ta Nijar murnar yadda dan takarar jam’iyyar su ta PNDS Bazoum Mohammed ya zaben.

Da yammacin Talatar nan ne dai hukumar zaben kasar Nijar CENI ta sanar da cewa Bazoum Mohammed ne ya lashe zaben shugaban kasar da kaso 55.75, inda ya kayar da abokin karawarsa na jam’iyyar RDR Tchanji Mahamane Ousmane.

Shugaba Buhari ya bukaci fusatattu daga cikin wadanda suka fadi zabe, da su bi hanyoyin da doka ta tanadar, don kada su yanke hukunci da kansu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply