Home Labarai Buhari ya jajanta kan harin Boko Haram na Auno tare da barazanar...

Buhari ya jajanta kan harin Boko Haram na Auno tare da barazanar daukar kwakkwaran mataki

78
0

Shugaba Buhari ya jajantawa iyalan wadanda harin kauyen Auno da ke babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri tare da bada tabbacin gwamnatin sa na kawo karshen ayyukan kungiyar ta Boko Haram.

Wata sanarwa da mataimakin shugaban kan yada labarai Garba Shehu ya fitar, Buhari ya yi tir da mummunan harin da aka kai kan ‘yan Nijeriyar da ba su jiba, basu gani ba.

A cewar sa, gwamnatin sa a shirye take wajen kuntutawa duk wani yinkuri na ‘yan kungiyar na haifar da rashin tsaro a kasar.

Buhari wanda ya jajantawa gwamnatin jihar Borno kan harin, ya gargadi ‘yan ta’addar da cewa dubun su ta kusa cika.

Harin na Auno, wanda aka kai da misalin karfe 9:45 na daren Lahadi ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 30 wadanda mayakan Boko Haram suka dira kan motocin su tare da cinna masu wuta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply