Home Labarai Buhari ya jinjinawa Atiku, Ɗangote, BUA da wasu

Buhari ya jinjinawa Atiku, Ɗangote, BUA da wasu

129
0

Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjinawa wasu ƴan Nijeriya kan gudunmuwar da suke badawa a yaƙin da ake da coronavirus a ƙasar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa ya fitar yau Juma’a, Buhari ya godewa haɗadɗiyar ƙungiyar ɓangarori masu zaman kan su da ke yaƙi da Covid-19.

Ya jinjinawa ƴan ƙungiyar musamman irin su Aliko Ɗangote, Abdulsamad Rabi’u mai BUA, Femi Otedola, Tony Elumelu, Herbert Wigwe, Segun Agbaje da Jim Ovia mai UBA, bankunan Access, GTB, da Zenith kan bada gudunmuwar Naira Biliyan 1 da suka yi.

Ya kuma yaba masu da ƙarfafa gwiwar sauran ɓangarori masu zaman kansu da suka yi na suma su bada irin wannan tallafi.

Buhari ya yi bayanin cewa UBA ya bada gudunmuwar ₦5bn ga Nijeriya da Afirika, sai tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ya bada ₦50m.

A cewar sa, bankin First Bank na haɗin gwiwa da gwamnati da kuma majalisar Ɗinkin Duniya da kamfanonin fasahawa wajen samar da hanyar karatu ta intanet ga kimanin yara miliyan ɗaya.

Fadar shugaban ƙasar ta kuma godewa duk wasu mutane da ƙungiyoyj da suka bada gudunmuwar su a sirrance, tare da yin fatan Allah ya saka masu da alkhairi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply