Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori Babban Daraktan hukumar daukar ma’aikata ta kasa NDE, Nasiru Argungu.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban ƙasar, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Talatar.
Sanarwar ta bayyana cewa tuni shugaba Buhari ya umurci karamin Ministan kwadago da samar da ayyuka, Mista Festus Keyamo, ya nada mukaddashin babban darakta daga manyan daraktocin hukumar don maye gurbin Argungu.
To sai dai kuma cikin sanarwar sallamar Argugu ba a bayyana dalilin sallamar ta sa ba.
