Home Sabon Labari Buhari ya lalata kasar nan-Sheik Gumi

Buhari ya lalata kasar nan-Sheik Gumi

69
0

[cmsmasters_row][cmsmasters_column data_width=”1/1″][cmsmasters_text]

Fitaccen malamin addinin musulumcin nan da ke Kaduna Sheikh Ahmad Gumi, ya ce shugaba Buhari bai yi wa Nijeriya wani abin a zo a gani ba, illa ma ruguza kasar da ya yi.

Sheikh Ahmad Gumi da ya yi wannan furucin a lokacin da ya karbi bakuncin wani malamin addinin Kirista Isa el Buba a gidansa ya ce illar da Shugaba Buhari ya yi a bangaren tattalin arziki na iya daukar shekaru 40 kafin a gyara ta.

Jaridar Vanguard ta ruwaito Sheikh Gumi yana cewa zaben da aka yi wa Shugaba Buhari shi ne mafi yawan magudi a cikin tarihin zabukan da aka taba yi a Nijeriya, inda kididdigar da ya samu ta nuna mutane kalilan ne suka samar da miliyoyin kuri’u a zaben.

Sai dai kuma jaridarmu ta DCL Hausa ta tuntubi Malam Sani Malumfashi daya daga cikin manyan daliban  Sheik Ahmad Gumi ya tabbatar da cewa Sheik Gumi ya ce kasar nan ta shiga mawuyacin hali a bangaren tattalin arziki a sakamakon wasu manufofi da gwamnatin shugaba Buhari ta fito da su. Amma kuma ya musanta cewa fitaccen malamin ya yi maganar sahihancin zaben shugaba Buhari da wata jarida a baya-baya nan.

A nasa bangaren malamin addinin Kiristan Isa el Buba ya yaba wa Shekh Ahmad Gumi a irin abin da ya kira jajircewa wajen tsage gaskiya komai dacinta.

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply