Home Sabon Labari Buhari ya maye gurbin shugabannin hukumomin da aka naɗa ministoci

Buhari ya maye gurbin shugabannin hukumomin da aka naɗa ministoci

144
0

Nuruddeen Ishaq Banye

Shugaban ƙasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya amince da naɗin waɗanda za su maye gurbin shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya da aka naɗa muƙamin ministoci.

 

Kamar yadda babban mai taimakawa shugaban ƙasar kan harkokin yaɗa labarai Garba Shehu ya bayyana, an naɗa Basheer Garba Mohammed a matsayin babban kwamishinan hukumar kula da ƴan gudun Hijira ta ƙasa wanda zai maye gurbin Sadiya Umar Farouk, sai kuma Dr Chioma Ejikeme da zai maye gurbin Sharon O. Ikeazor a matsayin babban sakataren hukumar tsara fansho.

 

Haka kuma, Garba Shehu ya ce an naɗa Kashifu Inuwa Abdullahi a matsayin babban daraktan hukumar kula da ci gaban fasahar sadarwa ta zamani, wanda zai gaji Dr Isah Ali Pantami.

 

A muƙamin kwamishinan kula da masu ruwa da tsaki na hukumar sadarwa ta ƙasa NCC kuwa, shugaba Buhari, ya aike da sunan Adeleke Moronfolu Adelewu ga majalisar Dattawa domin tabbatar da shi a matsayin wanda zai gaji Sunday Akin Dare.

 

A cewar Shehu, waɗannan naɗe-naɗe sun fara aiki ne nan take.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply